Iran:Takunkumin Amurka Kan Iran Ta’addancin Tattalin Arziki Ne

jakadan iran a mdd yayi tir da takunkumin amurka kan jirage 27 na iran kuma yace taadancin tattalin arziki ne

Gulamhussain Darzi wakilin iran a majalisar dinkin duniya a cikin wata wasika da ya aikewa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya fadi cewa kakaba takunkumin kan kamfanonin jiragen sama guda 27 na kasar iran da kasar Amurka ta yi, shi ne hakikanin Ta’addancin tattalin arziki, kuma take hakkin dan adam ne da kuma keta dokokin majalisar dinkin duniya da hakkin dan  adam daya lizimta  kare fararen hula.

A jiya laraba ne wakilin kasar iran din ya aike da wasika ga sakatare janar din majalisar dinkin duniya da kuma shugaban kwamitin tsaro inda ya bayyana cewa haramta kamfanonin jiragen sama na kasar iran zai hana musu damar samun wasu bangarorin jirgin sama da wasu kayayyakin gyara da kula da jirgin saman da ake bukata, wanda haka zai jefa matafiya da ma’aikatan kamfanonin cikin hadari kuma zai takaita zirga-zirgar miliyoyin fararen hula.

Haka zalika babban jami’in diflomasiyar ya kara da cewa wannan matakin ya take dokokin kasa da kasa na shari’a da aka amince da shi a ranar 3 ga watan oktoban shekara ta 2018, kotun ta yi nazari sosai kan tasirin da matakin amurka zai yi akan tsaron jiragen sama da kuma rayukan matafiya, sanan kuma ta umarci Amurka da ta nisanci duk abin da zai iya kawo cikas dake tattare da fitar da kayayyaki a kasar Iran, da suka zama dole ga tsaron jiragen sama

Daga karshe ya bukaci sakatare janar din majalisar dinkin duniya da shugaban kwamitin tsaro da su dauki matakin dakatar da matakin bangare da ya sabama doka da kasar Amurka ta dauka , da kuma wuce gona da iri da take yi kan kasar iran da yake shafar fararen hula ,kuma tayi aiki da dukkan alkawuran da ta dauka da yayi daidai da dokokin kasa da kasa ba tare da yin togiya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted