Tashar talabijin din CBS ta Amurka ta bayar da labarin da yake cewa; Martani mai tsanani da Iran ta kai saboda kai wa jiragen ruwanta na dakon man fetur, ya yi sanadiyyar lalata jiragen yakin Amurka 9 a kasar Jordan.
Rahoton tashar talabijin din ta Amurka ya tabbatar da cewa hari da makamai masu linzami da Iran ta kai ne a sansanin sojan saman a “Muwaffaq al-suldhi” dake kasar Jordan ne ya lalata jiragen yakin na Amurka guda 9. Daga cikin nau’oin jiragen da su ka lalace da akwai samfurin A-10 Thunderbolt II wanda sojojin Amurkan ke amfani da shi domin bayar da kariya ga soja kasa a filin daka. Daya daga cikin fika-fikan ya tarwatse saboda bugun da makaman Iran masu linzami su ka yi masa. Sai kuma jirgin F-15 wanda shi ne ya illata saboda harin na Iran.
Bugu da kari, hare-haren na Iran akan cibiyoyin Amurka ya shafi sansanonin “Yarima Hassan” da kuma ‘Azraq”.
Kafafen watsa labaru da dama sun nuna yadda makamai masu linzami su ka rika saukar Ruwan sama akan sansanonin na Amurka dake kasar Jodan, tare da bayyana shi a matsayin mafi girma tun bayan tsayawar yaki gadan-gadan.
Harin na Iran dai yana a matsayin mayar da martani ne akan harin da Amurka ta kai wa jiragen ruwa na dakon man fetur da Iran.
Iran dai ta sha nanata cewa kowane hari da za a kai mata sai fuskanci mayar da maartani mai tsanani akan sansanonin abokan gaba.