Dakarun “Kassam” Suna Alhinin Shahadar Daya Daga Cikin Kwamandojinta Farah Hamid

Dakarun rundunar “Kassam” na kungiyar Hamas ta Palasdinu sun sanar da shahadar mamba a cikin majalisar jihadi Farah Ahmad Abdulmajid Hamid wanda ya fuskanci kisan

Tambarin Kassam

Dakarun rundunar “Kassam” na kungiyar Hamas ta Palasdinu sun sanar da shahadar mamba a cikin majalisar jihadi Farah Ahmad Abdulmajid Hamid wanda ya fuskanci kisan gilla a hannun ‘yan sahayoniya a yammacin Gaza.

Dakarun na “Kassam” sun sanar da cewa; Hamid wanda ake kira da sunan; “Abu Ahmad” ya tafiyar da rayuwarsa ne a cikin gwagwarmaya, kuma yana cikin ‘yan Kassam da su ka kai hare-hare har sau tara a yammacin kogin Jordan a yayin boren “Aqsa” wanda ya halaka ‘yan sahayoniya 9 da mafi yawancinsu sojoji ne.

 Sanarwar ta Kassam ta kuma ce bayan yarjejeniyar musayar fursunoni da ‘yan sahayoniya wacce ake kira da “Wafa’ lil ahrar.” Bayan an  sake shi daga kurkuku ne ya bar yammacin kogin Jordan zuwa yankin Gaza. A can ne ya rika rike mukamai a karkashin gwgawarmaya har zuwa lokacin shahadarsa.

 Dakarun na Kassam sun bayyana cewa; Sahahdar Hamid ba za ta dakatar da tafarkin gwgawarmaya ba, tare da yin alkawalin ci gaba da tafiya a wannan godaben duk da girman sadaukar da kan da ke tattare da shi.

A jiya Laraba ne Farah Ahmad Hamid al-Nadhuri ya yi shahada a Gaza bayan da sojojin sahayoniya su ka kai masa hari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted