Rahotanni da suke fitowa daga kasar Yemen sun ce mayakan Ansarullah sun kutsa cikin garin ” Makha” mai muhimmanci saboda yadda yake da kusancin kilo mita 40 daga mashigar Ruwan Babal Mandab na tekun “Red Sea”.
Hukumar Yemen ta birnin Aden wacce Saudiyya take goya wa baya, ta sanar da cewa sun janye sojojinsu daga yankin domin sake tsara dabarun yaki.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar gwamnatin ta Aden tana tabbatar da cewa; Ansarullah sun shiga garin na Mukha, sun kuma shimfida ikonsu a cikinsa.
Abinda ya faru babban koma baya ne ga Saudiyya da kuma gwamnatin Aden da take goyawa baya.