Sharhin Bayan Labarai: Hukumar IAEA Zata Mai Iran Kwamintin Tsaro

Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Shirin Maida shirin makamashin Nukliyan kasar Iran zuwa kwamitin Tsaro na MDD”. Wanda

Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Shirin Maida shirin makamashin Nukliyan kasar Iran zuwa kwamitin Tsaro na MDD”. Wanda ni tahir amin zan karanta.

///….Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da gwamnonin hukumar makamashin nukliya ta Iran suka samar da nufin sake maida batun shirin makamashin nukliya na kasar Iran zuwa kwamitin tsaro na MDD a yau Laraba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ofishin jakadancin kasar Iran a cibiyoyin majalisar duniya dake Vienna yana fadar haka a shafinsa na X a safiyar yau Laraba.

Ofishin jakadancin ya fidda wannan sanarwan ne bayan da gwamnonin hukumar ta IAEA suka amince da kudurin nuna kiyayya da JMI a yau Laraba, wanda kasashen Amurka Burtania Faransa da kuma Jamus suka gabatar, wanda kuma bayan kada kuri’u kasashe 23 suka amince da kudurin a yayinda  kasashen 3 Rasha China da kuma Niger suka ki amincewa, sai kuma sai kuma kasashe 8 suka ki kada kuri’unsu.

Kudurin ya bukaci babban sakataren hukumar da IAEA Rafael Grossi ya gabatar da Iran a gaban kwamitin tsaro na MDD da kuma babban zauren MDD tare da tuhumar Iran da rashin mutunta al-kawulan da ta dauka dangane da shirinta na makamashin nukliya a karon farko fiye da shekaru 20 da suka gabata.

Ofishin jakadancin Iran a Vienna ya kara da cewa wannan kudurin ya nuna irin yanda hukumar ta ke biyewa yan siyasa a duniya ba tare da yin aikin da ya wajaba a kanta ba. Da haka kuma tana rusa matsayinta da muhimmancita a duniya.

Iran dai ta aza laifin tabarbarewar dangantakar ta da hukumar ta IAEA kan Amurka da HKI wadanda suka farwa kasar da yaki, sannan a cikin watan Yunin shekara ta 2025 suka kai hare hare kan cibiyoyin Nukliyar kasar da suke Fordo Natanz da kuma Esfahan.

Kuma Amurka da HKI ne suka jagoranci samar da wannan kudurin a halin da ake ciki a yanzu.

Ofishin ya kara da cewa, Washington ba zata taba kaiwa ga manufofinta a kan kasar Iran ba, na mika kai ga bukatunta, tare da yaki da kuma kwace dokiyoyinta a cikin shekaru kimabi biyu da suka gabata. Tare da amfani taimakon kawayenta da kuma da kuma yanta’addan da ta samar a yankin yammacin Asiya don cimma manufofinta.

Yace Amurka da HKI sun yi ruwan boma bomai kan cibiyoyin Nukliya wadanda suke karkashin kula na hukumar IAEA wacce kuma ta tabbatar da rashin karkatan shirin zuwa samar da makamai. Hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa dangane da hakan.

Bayanin ya yi tir da yakin da wadannan kasashe biyu suka dorawa JMI kimani watanni 6 da suka gabata, wanda aka ciki suka aikata laifukan yaki wadanda suka hada da kissan fararen hula da dama daga ciki har da yan makarantar Shajaratu Attayyibah na garin Minab da malamansu 168. Da kuma bom da suka jefa a kan bakin bikin aure a wani kauye kusa da tekun farisa.

Daga karshe ofishin ya kammala da cewa hukumar IAEA ba zata taba samawa Amurka da HKI nasara a kayen da suka sha a hannun sojojin Iran a wannan yakin ba. Sun sha kasa har’abada, ba zasu kuma maida mutuncinsu a duniya ba.

A dayan bangaren kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Kazen garib Abadi ya bayyana cewa rashin amincewa ma’aikatan hukumar su dawo Iran don ci gaba da bincike a wadannan cibiyoyi, yana da nasaba da yakin da kasashen yamma suke fafatawa da kasar Iran. Don haka itama tana taimaka masu a yankin ne.

Yace:  Sun faraway kasar Iran da yaki, suka kawo cikas a aikin da hukumar IAEA take gudanarwa a Iran, sannan suka gabatar da hakan a matsayin laifi a kan kasar Iran. Suka kuma dora mata laifin hana bincike”. Wannan dabarar ba zata yi aiki kan Iran ba injishi.

Ya ce, tare da siyatantar da aikin hukumar IAEA , gwamnonin ba zasu cimma manufofinsu ba ko a kwamintin tsaro na MDD ko kuma a babban zauren MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted