A wani bayani na hadin gwiwa da kasashen China da Rasha su ka fitar sun ce; Daftarin kudurin da kasashen turai uku ( Jamus, Faransa da Birtaniya) su ka gabatar da majalisar alkalai ta hukumar makamashin Nukiya ta duniya ( IAEA), wanda yake nufin kai shi gaban kwamitin tsaron MDD, ba shi da madogara ta doka.
Bayanin na kasashen China da Rasha ya kuma ce; matakin yana nufin kara dagula al’amurra kuma bai dace ba da siyasar da kasashen suke maganar aiki da ita ba, ta aiki da diplomasiyya.
Bugu da kari kasashen sun yi kira ga kasashe mambobi da su yi nazarin sakamakon da wannan matakin nasu zai iya haifarwa, su janye goyon bayansu ga kudurin.
Har ila yau kasashen na China da Rasha sun ce zargin da aka yin a cewa Iran ba ta aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta, siyasa ce da ba ta dogara da wani kwakkwaran dalili ba.
Haka nan kuma bayanin ya yi tir da hare-haren da aka kai wa cibiyoyin Nukiliyar Iran wadanda suke a karkashin sa ido da kulawar hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa.
A karshen bayanin an yi kira da a kawo karshen duk wani yanayi da hali na yaki matukar ana son a warware dukkanin matsalolin da ake fuskanta.