MDD Ta Tabbatar Da Rabuwar Kai A Kwamitin Tsaro Kan Takunkuman Majalisar A Kan Iran

Mataimakin babban sakataren MDD kan al-amuran siyasa Rosemary DiCarlo ta bayyana cewa kwamitin ya rabu gida biyu dangan da sake farfado da kudurin MDD mai

Mataimakin babban sakataren MDD kan al-amuran siyasa Rosemary DiCarlo ta bayyana cewa kwamitin ya rabu gida biyu dangan da sake farfado da kudurin MDD mai lamba 2231 kan shirin Nukliyar kasar Iran da kuma shirin ‘Snapback’ da ke cikinsa.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, shirin Snapback dai wani shiri ne a cikin yarjeniyar JCPOA ta shekara ta 2015 wanda ya bada dama a sake farfado da dukkan takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa Iran kafin yarjeniyar ta JCPOA idan har Iran din ta ki da aiwatar da abubuwan da suke cikin yarjeniyar.

Amma abin yake faruwa kasashen yamma Musamman Amurka da Burtania da faransa sune suka fara karya yerjeniyar, inda Amurka ta fice daga cikinta a shekara ta 2018 sannan kasashen Turai wadanda suka hada da Burtania da Faransa da kuma Jamus duk sun ki su aiwatar da abubuwan da suka hau kansu a cikin yarjeniyar. A lokacinda Iran ta ga haka ita kuma ta maida martani da tace makamashin yuranium har zuwa kasha 60 % wanda ya sabawa yarjeniyar.  Sannan bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan Yunuin da ya gabata kasashen Turai Uku Faransa da Jamusa da kuma Burtania sun yi kokarin amfani da shirin Snapback da ke cikin yarjeniyar JCPOA don sake maida takunkuman MDD kan Iran al-ahali su suka fara yin watsi da shi. Sai dai sun kasa yin hakan har zuwa watan octoban wannan shekarar a lokacinda kudurin MDD mai lamba 2231 da kuma yarjeniyar ta JCPOA gaba daya suka mutu aka kuma rufe batun shirin nukliyar kasar Iran kwata kwata a Kwamitin Tsaro.

Amma a taron Kwamitin tsaron a jiya wadannan kasashen sun so su sake farfado da kudurin, amma suka kasa saboda rabuwar kai a cikin kwamatin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted