MDD Ta Gudanar Da Bikin Nuruz Ta Kasa Da Kasa

An gudanar da bukukuwan ranar Nuruz, ko ranar farko ta hijira shamsiyya ta Iraniyawa da kasashe makobta a Majalisar dinkin duniya a jiya Laraba a

An gudanar da bukukuwan ranar Nuruz, ko ranar farko ta hijira shamsiyya ta Iraniyawa da kasashe makobta a Majalisar dinkin duniya a jiya Laraba a daya daga cikin zaurukan majalisar a birnin NewYork cibiyar MDD a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bikin Nuruz na bana wato shekara ta 1403 ya sami halattar Jakadun kasashe 12 da wasu jami’an diblomasiyya na kasashen duniya. Har’ila yau taron ya sami halattar shugaban babbau zauren majalisar dinkin duniya.

Labarin ya kara da cewa Amir Saeed Iravani jakadan JMI na din din din a MDD tare da tolwarorinsa daga kasashen 11 ne suka jagoranci bukukuwan Nurus na wannan shekarar. Har’ila yau tare da su akwai shugaban hukumar UNESCO, shugaban babban zauren MDD a taron.

Jakadun sun hada da kasashen Afghanistan, Iran, Iraq, India, Kazakhstan, Pakistan, Kyrgyzstan, Turkmenistan, Uzbekistan, Azerbaijan, da Turkiyya. Har’ila yau wadannan kasashe sune ake bubukuwan nuruz a cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments