Babban jami’in MDD mai kula da ayyukan jin kai James Mcgoldrick ya ce; Halin da ake ciki a yankin Gaza yana tattare da matsananciyar damuwa, domin mazaunansa suna gab da fadawa cikin yunwa ta bai daya.
Jami’in na MDD ya kuma bayyana cewa;kananan yaran yankin kuwa suna fada da rashin abinci mai gina jiki da ba a taba ganin irinta ba.
Har ila yau Mcgoldrick ya bayyana yunwa da ake amfani da ita a matsayin wani bom wanda ba a jin karar jefa shi da faduwarsa.
Dama a baya kakakin Asusun Kananan Yara na MDD, ( UNICEF) Jmane al-Dur, ya bayyana cewa da akwai kananan yara 100,000 da suke fama da yunwa a yankin Rafah.
Ita kuwa hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta ce, rashin abinci a Gaza ya yi tsanani sosai.