Majiyoyin Majalisar Duniya sun tabbatar da cewa motoci da dama na kungiyoyin agaji sun tsallaka zuwa Sudan daga kan iyakar Adre da Chadi domin kai kayan agaji a yankunan Darfur da ke fuskantar barazanar yunwa.
”Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce motocin suna ɗauke da hatsi da dawa da man girki da kuma shinkafa waɗanda za su amfani kimanin mutum 13,000 da ke fuskantar barazanar yunwa a yankin Kereneik da ke yammacin Darfur,” kamar yadda mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya shaida wa kafar yada labarai ta New York a ranar Laraba.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya ta yaba da wannan mataki, tana mai cewa muhimman kayayyakin agajin da aka kai za su tallafa wa mutane sama da 12,000 masu buƙatar agaji.
Majalisar mulkin Sudan ta fada a ranar Alhamis ɗin da ta gabata cewa za ta ba da damar wucewa ta hanyar kan iyakar Adre da Chadi har na tsawon watanni uku – matakin da ƙungiyoyin agaji suka jima suna jira.
Masu sa ido a duniya sun ce sama da mutum miliyan shida ne ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci a fadin yankin Darfur, wanda mafi akasari ke ƙarkashin ikon dakarun rundunar sa kai ta RSF da ke adawa da sojojin ƙasar a yakin da aka shafe tsawon watanni 16 ana gwabzawa, kana yunwa ta yi ƙamari a sansanin Zamzam da ke arewacin Darfur.
Gwamnatin da ke da alaƙa da sojoji ta hana kai kayan agaji a watan Fabrairu ta hanyar Adre zuwa cikin yankin da RSF ke iko da shi, bisa zargin cewa ana amfani da hanyar wajen isar da makamai.
”Sake buɗe mashigar Adre yana da matukar muhimmanci ga kokarin daƙile yaduwar yunwa a Sudan, kuma dole ne a ci gaba da amfani da ita. Ina so na jinjinawa duka bangarorin da suka ɗauki wannan muhimmin mataki na taimaka wa WFP wajen samun damar kai agajin ceton rai ga miliyoyin mutanen da ke cikin matsanaciyar buƙaka,” in ji babban Darakta WFP Cindy McCain.
Shirin samar da abinci na duniya zai ci gaba da amfani da hanyar Adre daga Chadi kana ita ce hanya mafi sauƙi wajen isar da kayan agajin jinƙai zuwa ga Sudan, musamman yankin Darfur, la’akari da ma’auni da saurin da ake buƙata don tunkarar matsalar yunwa.
Daga Adre, manyan motoci na iya tsallakawa zuwa Darfur kuma su isa wuraren rarraba kayayyaki a cikin rana guda.