Mazauna yankunan karkara na kasar Tunisiya suna fuskantar matsalar rashin tsaftataccen Ruwan sha
A wani kauye mai tazarar kilomita goma daga birnin Jumen, mazauna yankin suna rayuwa ne kusan a kullum rana cikin bukatar muhimman abubuwan rayuwa musamman Ruwan sha.
Domin samun tsaftataccen ruwan sha, sai mata da tsofaffi sun yi tafiya mai nisa a kullum rana tare da ratsa cikin gonakin noma don samun rijiyar da zasu dibo Ruwan da zasu yi amfani da shi, inda ta zama wata alama ta matsananciyar matsalar ruwan sha da ake gani a yankin koren Tunisiya.
Yankuna da dama a kasar Tunusiya na fuskantar matsalar karancin ruwa wanda yake daukar tsawon sa’o’i ko kwanaki babu ruwa bisa la’akari da matsalar karancin ruwa da kuma raguwar madatsun ruwa sakamakon fari da kasar ke fama da shi, wanda ya rubanya wahalhalun da mazauna wadannan yankuna ke ciki.