Isra’ila Ta Yi Wa Shugaban Kasar Turkiya Barazanar Kisa

Ministan harkokin waje na HKI “Yisrail Kats” ya wallafa hoton shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan a shafin “X” sannan ya kuma rubuta cewa: Yana yi wa Isra’ila baraza, don haka mutuwa ce a gabansa.” Shi dai shugaban kasar Turkiya yana Magana ne akan abubuwan da suke faruwa a Falasdinu, inda ya bayyana cewa; Wajibi […]
Iran: Zaben Kasar Venezuela Yana Nuni Da Hakikanin Tsarin Demokradiyya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Msuulunci ta Iran Dr.Nasir Kan’ani ya wallafa a shafinsa na “X” sakon taya murna ga shugaba Nicolas Maduro da aka sake zabarsa a wani karo a matsayin shugaban kasar Venezuela, tare da cewa, saboda yadda mutane da dama su ka shiga yin zaben da kuma masu sanya idanu na kasa […]
Iran: Fadada Wuraren Da HKi Take Kai Wa Hare-hare Bazarana Ce Ga Tsaron Duniya

Babban jami’in diplomasiyyar Iran Ali Bakiri Kani ne ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Cigaba da fadada laifukan HKi a yankin Gaza, wata babbar barazana ce ga sulhu da zaman lafiya na duniya. Babban jami’in diplomasiyyar ta Iran ya bayyana haka ne a yayin da ya gana da mataimakin minstan harkokin wajen kasar […]
Maduro ya lashe zaben shugaban kasar Venezuela a wa’adi na uku

An sake zaben Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasar Venezuela domin yin wani sabon wa’adin shugabanci karo na uku, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar. Elvis Amoroso, shugaban hukumar zabe ta CNE, ya ce Maduro mai shekaru 61, ya samu kashi 51.2 cikin dari na kuri’un da aka kada jiya Lahadi, wanda ya tabbatar […]
‘Yan gwagwarmaya a Iraki sun gargadi Isra’ila kan shiga yaki da Lebanon

Kungiyar gwagwarmaya da kuma yaki da ta’addanci ta kasar Iraki ta yi gargadin cewa sabbin ka’idojin aikin za su yi wa Amurka da Isra’ila illa matuka idan har gwamnatin yahudawan Isra’ila ta zabi kaddamar da farmaki kan kungiyar gwagwarmayar Hizbullah bisa zargin kai hari da makami mai linzami a tuddan Golan na Syria da Isra’ila […]
Kungiyoyin Fafutuka sun gargadi gwamnatin Najeriya Kan yi Barazana ga masu Zanga-Zanga

A yunkurin da ake na gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da mawuyacin halin da jama’a suke cikia Najeriya, wasu kungiyoyin kare dan adan sun gargadi gwamnati yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zangar. Kiran zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, ta samu karbuwa a shafukan […]
Wasu likitoci sun gargadi gwamnatin Biden kan halin da ake ciki a Gaza

Wasu gungun likitoci da ma’aikatan jinya na Amurka sun rubuta budaddiyar wasika zuwa ga shugaban Amurka Joe Biden, inda suke nuna rashin amincewa da mummunan halin da ake ciki a Gaza. Wasu likitocin kasar Amurka sun aike da budaddiyar wasika zuwa ga Joe Biden, shugaban kasar Amurka, da kuma mataimakinsa Kamala Harris, kan abin da […]
Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Gungun Mabarnata Ne Masu Aikata Muggan Laifuka

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yahudawan Sahayoniyya a matsayin wasu gungun masu aikata muggan laifukan kashe-kashen rayuka kuma ‘yan ta’adda Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne sabuwar gwamnatin Iran ta kasance mai tasiri da rawar da take takawa dangane da batutuwan da suka […]
Kasar Turkiyya Ta Yi Barazanar Shiga Tsakani A Yakin Da Yahudawa Suke Yi Gaza

Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Kasarsa a shirye take ta tsoma baki kan abubuwan da haramtacciyar kasar Isra’ila take aikatawa kamar yadda ta yi a Karabakh da Libya Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa: Turkiyya na iya shiga tsakani kan ayyukan wuce gona da iri da haramtacciyar kasar Isra’ila ke […]
Kungiyar Hizbullah Ta Mallakin Sabbin Makamai Da Manyan Kasashen Yankin Ba Su Da Su

Kungiyar Hizbullahi ta mallaki wasu sabbin makamai wadanda manyan kasashen yankin ba su mallaka ba! Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta buga labarin da ta yi karin haske kan abin da jaridar “Al-Jarida” ta kasar Kuwaiti ta buga a ‘yan kwanakin nan, inda ta bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon […]
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Cewa: Ana Ci Gaba Da Tafka Muggan Laifukan Yaki A Gaza

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta jaddada cewa: Ci gaba da yakin Gaza laifi ne ga dukkan bil’adama Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Ci gaba da yakin Gaza da kuma kashe-kashe da raunata dubban daruruwan Falasdinawa, yakin wuce gona da iri ne da kuma laifi kan dukkanin bil’adama da kuma […]
Mazauna Yankunan Karkara A Tunusiya Suna Fuskantar Matsalar Rashin Tsaftataccen Ruwan Sha

Mazauna yankunan karkara na kasar Tunisiya suna fuskantar matsalar rashin tsaftataccen Ruwan sha A wani kauye mai tazarar kilomita goma daga birnin Jumen, mazauna yankin suna rayuwa ne kusan a kullum rana cikin bukatar muhimman abubuwan rayuwa musamman Ruwan sha. Domin samun tsaftataccen ruwan sha, sai mata da tsofaffi sun yi tafiya mai nisa a […]