Iran Ta Bukaci ICRC Ta Bi Kadin Matuka Jirgin Iran 3 A Qatar

Iran ta bukaci Hukumar Ba da Agaji ta Red Cross ta Duniya (ICRC) ta binciki makomar matuka jirgin yakinta uku da Tehran ta ce sun

Brigadier General Mohammad Bagherzadeh, kwamandan sojojin sama na JMI kuma mai kula da kwamitin mayakan da suka bace, ya rubuta wasika ga hukumar redcressen ta kasa da kasa  (ICRC) don bin Kadin matuka jirgin sama yaki na kasar Iran da suka bace a kasar Qatar bayan yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar a farkon wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto Janar Bagherzadeh yana cewa, ya rubutawa shugaban Red Cross ta duniya Mirjana Spotjari wasiki inda yake butar hukumar ICRC ta bi kadan neman wadan nan matuka Iraniyawa uku wadanda aka kamasu a raya a kasar Qatar a cikin yakin.

Labarin ya kara da  cewa Javad Salehi, Abdolmajid Dashtian, da kuma Omran Behraveshian, sun kai wasu hare hare ne a cikin kasar Qatar a cikin yakin, amma suna kan hanyarsu ta dawowa aka kakkabo jiragensu, daya daga cikinsu ya yi shahada, kuma har an dawo da gawarsa gida an masa jana’iza, amma sauran matuka jirgin guda uku iran tana da masaniya kan cewa an kamasu da ransu, amma har yanzu baba labarinsu.

A ranar 28 ga watan Fabrayru ne kasashen Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki daga kasashen larabawa na yankin tekun farisa, wannan yasa Iran ta ke maida martani a kan makiya a wadan nan kasashe. Da wannan dalilin suka aika wadannan matuka guda 4 zuwa kasar Qatar. Inda abinda ya faru ya faru da su.

Sai dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar Majid Al-ansari ya musanta cewa kasarsa tana rike da matuka jirgin yaki na kasar Iran guda uku.

Al-ansari ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya jiya Abasar ya kuma kara da cewa, kasar Qatar ta nemi wadanan matukan bata gansu ba, kuma ta rika ta mikawa Iran gawar daya daga cikin matuka jirgin samun yakin samfurin Su-24 da aka kakkabo a cikin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted