Araqchi: Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Har yanzu Iran ba ta yanke shawarar sake fara tattaunawa da Amurka ba Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Har yanzu Iran ba ta yanke shawarar sake fara tattaunawa da Amurka ba

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad (MOU) ta tanadar da kawo karshen yaki, ba tsagaita bude wuta ba. Ya bayyana cewa Amurka ta karya yarjejeniyar, wanda hakan ya haifar da sake barkewar rikici. Saboda haka, babu wani abu kamar tsagaita bude wuta na kwanaki 60 da zai buƙaci tsawaitawa.

Araqchi ya bayyana cewa: tsayar da tsawon kwanaki 60 baya nufin cewa an ware kwanaki 60 don tattaunawa da zai kai ga cimma yarjejeniya ta ƙarshe, don haka babu batun cewa; An tsayar da tsagaita wuta na kwanaki 60.

Ya ƙara da cewa masu shiga tsakani, Qatar da Pakistan, suna musayar saƙonni kuma suna hulɗa da su, amma wannan ba ya nuna tattaunawa ce, kuma har yanzu ba a yanke shawara ba game da sake fara tattaunawa da Amurka.

Dangane da tattaunawar da ke tsakanin Iran da Oman, ya ce, “Tattaunawa da Oman tana ci gaba, amma wannan batu ne na daban da ya shafi na fasaha game da tantance hanyoyin ruwa ta hanyar mashigar ruwa ta Hormuz don jigilar kaya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted