An Ji Karar Musayar Wuta A Kudancin Lebanon

Rahotanni sun ce an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin dakarun Hizbullah da sojojin HKI a kudancin Lebanon, yayin da aka kai hare-hare ta sama

A dai dai lokacinda HKI ta sabonta hare hare ta sama da makaman Atilary da kuma amfanin da makaman phosphorous a kudancincin kasar Lebanon  a daren jiya .

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto cewa sojojin HKI sun yi musayar wuta mai tsanani a daren jiya a waurare daban daban daga ciki har da kan tuddan Ali Alttahir kusa da lardin Nabathia a kudancin kasar.  Tankunan yaki da kuma makaman igwa duk sun yi barin wuta kan yanakin,

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa an yi musayar wuta mai tsanani a kan tuddan Ali Attahir a lardin Nabathiaa, kuma an yi amfani da makaman agwa a kan sa. Sun kuma yi amfani da makaman guba ta Phosphoros a kan mutanen yankin.

Wata majiya ta bayyana cewa dakarun kungiyar Hizbullah sun fafata da sojojin HKI a kan duddan don hanasu shiga. Sannan kafafen yada labaran Ebranci ya bada labarin cewa wasu yahudawan sun halaka ko sun jikada a fafatawar na jiya da dare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted