Mutane 10 Sun Yi Shahada A Hare-haren “Isra’ila” A Kduancin Lebanon

Sojojin  Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garin Ansar tare da yi wa mutane kisan kuashi, haka nan kuma a garuruwan Deir-Zahrani da Tallah

Hare-haren 'yan mamaya a kudancin Lebanon

Sojojin  Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garin Ansar tare da yi wa mutane kisan kuashi, haka nan kuma a garuruwan Deir-Zahrani da Tallah Ali Tahir da al-fuqah.

Wadannan hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da su ka hada da kananan yara, kamar kuma yadda wani adadi mai yawa na mutane ya jikkata.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa, mutane 7 sun yi shahada daga cikinsu da akwai kananan yara, sai kuma wasu mutane 2 da su ka jikkata a harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai da safiyar yau Asabar a garin Ansar a gundumar Nabadhiyyah.

Kamfanin dillancin labarum gwamnatin kasar ta Lebanon yta sanar da cewa; Sojojin na Isra’ila sun kai hari akan wani gida a kusa da garin na “Ansar” da shi ne sanadiyyar shahadar mutane 7.

Sanarwar ta kuma ce a garin Deir-Zahrani an sami shahidai 3 kamar yadda aka jikkata wasu mutane 7 a bisa kididdigar farko tare da yiyuwar karuwar adadin.

Kungiyoyin Agaji dai suna ci gaba da aikin tsamo gawawwakin shahidan da kuma wadanda su ka jikkata.

A can garin “Ali  Tahir” kuwa  jirgin yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne ya kai hare-hare har sau 8. Wadannan hare-haren kuwa an kai su ne akan cibiyoyin fararen hula mabanbanta na cikin garin da su ka haka makaranta da babban shatale-talen garin.

Tuni dai kungiyar Hizbullah ta yi  tir da abinda ya faru akan  wannan harin, tare da tabbatar da cewa za ta mayar da martanin da ya dace da girman harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted