Fiye da ‘yan jarida 40 ne aka fara bai wa horon soja a kasar Burkina Faso a karkashin Shirin da suke kira da ” Na Kishin Kasa.”
Gwamnatin shugaba Captain Ibrahim Traore wanda ya hau karagar Mulki tun a 2022, ya fito da tsarin bayar da horon soja ga ‘yan kasar da su ka hada ‘yan jarida a karkashin abinda ya kira “Shirin Kishin Kasa.”.
Ita dai kasar Burkina Faso da kuma makwabtanta Mali da jamhuriyar Nijar suna fuskantar hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda irin su alka’ida da ISIS ( Da’esh), masu ikirarin jihadi.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama a nahiyar ta Afirka sun fara yin suka akan wannan matakin na mahukuntan kasar ta Burkina Faso.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida ba tare da iyaka ba a yankin Kudancin Sahara Sadibou marong ya bayyana cewa:
” Wannan sabon Shirin yana tattare da damuwa akan ‘yancin aikin jarida.”
Haka nan kuma ya ci gaba da cewa; ‘Yan jarida ba sojoji ba ne, don haka bai kamata a mayar da su zama masu Magana domin kare yaki ba,a ce ana ba su makamai da kakin soja a jikinsu.”
Baya ga ‘yan jarida an kuma tilastawa daliban manyan makarantu yin horon soja wanda aka fara aiki da shi tun shekarar da ta gabata.
Da dama daga cikin kafafen watsa labaru masu zaman kansu a kasar ta Burkina Faso, an dakatar da su. Da akwai mata 44 a cikin ‘yan jaridar da ake bai wa horon na soja a kasar ta Burkina Faso.