Wani jami’in fadar white house ya bayyana cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump yana wargi ne a lokacinda ya fadawa masu sauraronsa a birnin NewsYork inda yaje yakin neman zabe, kan cewa idan ya sami nasar a kan Iran ya kwace mashigar ruwa ta Hurmuz to zai maida ita mallakin Amurka.
Brian Schwartz, dan jiridar World Street Journald a fadar white house ya nakalto wani jami’an fadar white House yana ce wa, Trump yana wargi da wasa ne da wadannan maganganun, saboda babu inda aka tattauna wannan batun da shi.
A maida martani jami’an gwamnatin kasar Iran sun fadawa Trump kan cewa, bai isa ya kwace mashigar ruwa ta Hurmuz ba, da makamai ko tweeter ko kuma jawabi a gangamin neman kori’a a New York.