Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya yi magana game da koma-baya da Trump ya yi kan bude mashigar Hormuz
Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya yi magana game da koma bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yarjejeniyar Iran ta bude mashigar Hormuz bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna.
Qalibaf ya bayyana a wani taro da wasu manyan mutane na al’adu cewa: “Sun dakatar da komai bayan harin da suka kai kwanan nan a yankunan kudancin Beirut, inda suka kashe shugaban hukumar leken asiri ta Kungiyar Hizbullah da iyalansa. Iran ta ce za ta kai musu hari a wannan daren, kuma idan Yahudawan Sahayoniyya suka rama, to Iran za ta kai hare-hare a duk yankunan Yahudawa da suke kan iyaka.”
Ya kara da cewa, “Sakamakon tattaunawar Iran shi ne dage takunkumin a wannan daren, ba kwana talatin bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ba. A wannan daren, Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa za su dage takunkumin a wannan daren, sannan ya rubuta cewa Iraniyawa za su bude mashigar Hormuz. Da Iran ta ga haka, ta dakatar da kai harin amma babu irin wannan yarjejeniyar a tsakaninsu. Qalibaf ya sanar da su cewa, idan ba goge wannan sakon nan take ba, wato zata kai hari da irin karfin da ta yi barazana.”
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya fayyace cewa ya kamata a duba ranar; Bayan mintuna 58, Trump ya goge sashe na biyu na sakon Twitter din sannan ya rubuta cewa za a bude tashar jiragen ruwa daga ranar Asabar a matsayin wani bangare na yarjejeniyar fahimtar juna.