Shuhada: A Kawo Karshen Mamayar Tattalin Arzikin Iraki

Babban sakataren kungiyar Kata’ib Sayyid al-Shuhada ta Iraki ya bukaci a kawo karshen abin da ya bayyana a matsayin mamayar Amurka kan tattalin arzikin kasar,

Babban sakatarin kungiyar dakarun sayyidu shuhada na kasar Iraki ya bukaci a kawo karshen mamayar da Amurka takewa tattalin arzikin kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto babban sakataren dakarun sayyidushuhada yana fadar haka a shafinsa na X ya kara da cewa, “mamayar hanyoyin samun kudade na kasar Iraqi musamman man fetur da Amurka ta ke yi, ya nuna cewa, gwamnatin kasar bata da cikekken iko a kan tattalin arziki da kuma kudaden kasar, wanda kuma yake tauye matsayin matsayin gwamnatin, mai cikekken yenci.

Abu Alaa Al-walaei ya kara da cewa kasar Iraki tana karkashin mulkin mallaka na kasar Amurka. Yace idan munason karban iko da kasarmu to dole ne mu nemi hanyoyin da zamu dawo da ikon kudademmu da tattalin arzikimmu a hannummu daga hannun kasashen waje musamman Amurka.

Daga karshe ya bayyana cewa, yencin kai ba zata samu ba sai tare da iko da dukkan abinda ya kasance na kasarmu ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted