A dai dai lokacinda kasar Iran take fama da matsin tattalin arziki daga kasar Amurka da kuma kasashen yamma, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, gwamnonin larduna na kan iyaka da kasashe makobta 15, su karfafa huldar kasuwanci da tattalin arziki da wadan nan kasashen makobta don rage tsaurin takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa, kasashe makobta sune babban damar da muke da shi na kyautata tattalin arziki a tsarin harkokin kasashen waje da muke da shi a halin yanzu.
Ministan ya bayyana haka ne a wani taro na musamman da Jami’an gwamnatin kasar wadanda suke kula da al-amuran yawon shakatawa da kuma ayyukan hannu a lardin Khurasan razawi.
Taron ya sami halattar ministan al-adu yawon shakatawa da kuma ayyukan hannu. Sayyed Reza Salihi-Amiri, ministan tattalin arziki da kudade, Sayyed Ali Madani, gwamnan lardin Khurasan Razawi Gholamhossain Muzaffari, sai kuma Ali-Asghar Shalbafiyan shugaban sashen zuba jari da tattalin arziki a ma’aikatar al-adu da adana kayakin tarihi.