Shugaba Pezishkiyan Ya Aike Wa Da Shugaban Gwamnatin Indiya Sakon Murnar Samun ‘Yancin Kasar

Shugaban kasar Iran Mas'ud Pezisehkiyan ya aika wa da Fira Ministan kasar Indiya Nyendra Mudi sakon taya kasar samun 'yanci daga mulkin mallakar Birtaniya sghekaru
Shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezisehkiyan ya aika wa da Fira Ministan kasar Indiya Nyendra Mudi sakon taya kasar samun ‘yanci daga mulkin mallakar Birtaniya sghekaru 79 da su ka gabata.

 Sakon da shugaban kasar ta Iran ta aikewa da Fira ministan kasar Indiya,ya kunshi cewa; lokacin tunanawa da samun ‘yancin dama ce ta bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu, kuma tsohuwar alakar da suke da ita ta fuskokin al’adu, tarihi da ci gaban suna a matsayin madogara da za a gina akai.

Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce; Iran ta bangarenta tana cikin Shirin bunkasa wannan alakar a karkashin girmama juna domin kare manufofin al’ummun kasashen biyu.

A karshe,sakon na shugaba Pezishkiyan ya roki Allah madaukakin sarki da ya tabbatar da daukaka da ci gaban kasar, da kuma fatan ganin alakar kasashen biyu ta bunkasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted