Jaridar ta Amurka ta buga wani rahoto wanda yake cewa ba a yanzu ne jirgin dakon jiragen yaki na Amurka “Abraham Lincon” ya fada cikin matsala ba, ta faro ne tun lokacin da Iran ta fara kai hari a kasar Bahrain.
Jaridar ta ce, tun a farkon yaki ne da Iran ta kai wa cibiyar sojan Ruwan Amurka a Bahrain hari ya rusa wani sashe mai girma na kayan aiki da aika sakwanni da jiragen Ruwan suke amfani da su.
Haka nan rahoton ya ce, bayan da Iran ta rusa kayan aikin da jiragen Ruwan na Amurka suke amfani da su a Bahrain, Amurkan ta koma amfani da cibiyarta dake Diego Garcia, ta Birtania mai nisan kilo mita 2200 daga tekun Oman.
Sai dai kuma duk da haka, amfani da cibiyar mai nisa daga inda jiragen yakin na Amurka suke, ya sa an sami karancin wasu kayan aiki da ake da bukatuwa da su a cikin jirgin na ” Abraham Lincol. Haka nan kuma ma’aikan da suke cikin jirgin Ruwan da sun kai 5000,gwiwowinsu sun yi sanyi.
A can Amurkan dai an fara cece-kuce a tsakanin ‘yan majalisar dattijai da kuma ma’aikatar yaki saboda halin da sojoji da sauran ma’aikatar jirgin Ruwan suke ciki.
Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai kafafen watsa labarun Amruka su ka fara korafi akan halin dake ciki a jirgin Ruwan na Abraham Lincol. Jaridar Guardian ta buga wani rahoto wanda yake cewa; sojojin Ruwan Amurka dake kan jirgin Ruwan “Abraham Lincol” da su ka dade akan doron ruwa sun yi kokarin kashe kawukansu ta hanyar yunkurin jefa kansu cikin ruwa.