Dubban masu zanga zanga da siyasar yaki da gwamnatin Binyamin na tanyaho ke yi ne suka rufe manya tituna a birnin Telaviv domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da yaki da take yi a yankin gaza bayan da ta kasa kubutar da yahudanwa da da kungiyar Hamas take rike da su.
Wannan zanga zangar tana zuwa ne bayan da isra’ila ta aike da wata tawaga zuwa kasar Qatar don tattaunawa kan batun yakin Gaza, da kuma yaiyuwa dakatar da bude wuta, masu zanga-zangar suna dauke da kyallye da wasu kwalaye da aka rubuta cewa kada ku dawo gida daga Qatar ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ya sanar cewa yazuwa yanzu yayi gaggawa a fara ace wani abu game da ci gaban da ake samu a tattaunawar da kae yin a batun tsagaita bude wuta kan yakin gaza amma dai muna da kyakkyawan fata akan lamarin.