Masifar yunwa da ta kunno kai a Zirin Gaza musamman yadda take addabar mata da kananan yara ta lashe rayukan yara 49 a baya-bayan nan
Kafofin yada labaran gwamnati a Gaza sun yi gargadin karuwar yara da jarirai da ke mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma yunwa mai tsanani a yankin.
Yunwa tana yin barna ga al’ummar Gaza yayin da matakin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauka na ci gaba da killace yankin tare da hana shigar da kayan abincin tallafi da na kiwon lafiya cikin yankin suke kara ta’azzara lamarin.
Al’ummar yankin arewacin Zirin Gaza na korafin karancin abinci da ruwan sha da kuma katsewar magunguna da ake samu a kai a kai, lamarin da ke sa marasa lafiya da kananan yara da dama suna rasa rayukansu.
Wata mata daga Gaza ta ce: Sun shiga cikin kangin yunwa tun farkon farkon bullar yaƙin, kuma a halin yanzu suna fama da yunwa fiye da kima. Kamar yadda wani tsoho ya bayyana cewa: Lamarin yana da ban tausayi yadda jama’a suke fuskantar masifar yunwa saboda rashin abinci ga kuma luguden wuta kan mai uwa da wabi da ake yi kan jama’a.
Haka nan wata mace bafalasdiniya ta bayyana cewa: Su ‘yan yankin arewacin Zirin Gaza ne, kuma suna fatan mutuwa don kada su rayuwa cikin wannan wulakanci na rashin ci da sha.