Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar diflomasiyya 3 da na gwamnatin Somaliya a yau talata Masar ta aikewa kasar Somaliya kashin farko na taimakon soja cikin shekaru arba’in da suka gabata, a wani mataki da ake ganin zai kara ta’azzara rikicin tsakanin kasashen biyu da Habasha.
Masar da Somaliya sun kara karfafa dangantakarsu a bana, bayan da Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta farko da yankin Somaliland mai ballewa daga kasar, wanda ya shafi bayar da hayar filayen ruwa a gabar teku, domin samun amincewar ‘yancin kai na Somaliland daga Somaliya.
Gwamnatin Mogadishu ta yi Allah wadai da yarjejeniyar da cewa wani hari ne ga diyaucinta, ta kuma sha alwashin dakile ta ta duk wata hanya da ta dace, inda ta kori jakadan Habasha tare da kiran nata zuwa Addis Ababa.
Ita ma Masar wadda ta dade tana takun saka tsakaninta da Habasha kan batun gina katafaren madatsar ruwa a kogin Nilu, ta kuma yi Allah-wadai da yarjejeniyar ta Somaliland.
A farkon wannan watan, Alkahira ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da Mogadishu, kuma ta yi tayin tura dakaru a wani bangare na sabuwar tawagar wanzar da zaman lafiya a Somaliya.
Tuni dai Somaliya ta yi barazanar korar dakaru 10,000 na kasar Habasha, wadanda suke can a matsayin wani bangare na aikin wanzar da zaman lafiya da kuma yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla na yaki da kungiyar ta’addanci ta al-Shabaab, matukar ba a soke yarjejeniyar ba.