Martanin Iran Ga Sambatun Donald Trump Akan Bude Mashigar Ruwan Hurmuz

A daren Lahadi ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake yin sambatu,irin wadanda ya saba akan Iran. A wannan karon, ya yi Magana

A daren Lahadi ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake yin sambatu,irin wadanda ya saba akan Iran. A wannan karon, ya yi Magana ne akan cewa daga safiyar Litinin jiragen yakin Amurka za su fara yi wa jiragen man fetur rakiya domin wucewa ta mashigar ruwan Hurmuz.Wannan irin sambatun ya fuskanci mayar da martani daga Iran tana mai gargadin cewa; kar Amurka ta kuskura ta ce za ta yi waw ani jirgi rakiya a wannan mashigar ruwa.

Shugaban kwamitin tsaron kasa da siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa; Babu yadda za a tfiyar da kuma kula da mashigar Hurmuz ta hanyar wallafa sakwanni a shafukan sada zumunta, kuma sakwannin da Trump din ya wallafa ba komai ba ne, sai mafarkin tsaye.

Shi dai shugaban kasar ta Amurka Donald Trump da ya wallafa wancan sakon ya kara da cewa; Wai za su yi haka ne bisa dalilai na ‘yan’adamtaka,kuma wai inda aka kai wa jragensu na yaki hari, to su ma za su bude wuta.

A dalilin haka ne  Ibrahim Azizi ya bayyana wannan irin yunkuri, idan har ya faru, to yana a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.

Ita kuwa babbar cibiyar sojan Iran ta “Khatamul-Anbiya” ta fitar da sanarwar cewa; Duk wani jirgin Amurka da ya karato mashigar Hurmuz zai fukanci bude wuta.

 Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa; Tsaro da kula da mashigar ruwan Hurmuz yana hannu Iran ne, don haka duk wanda yake son ya ratsa ta wajen,to dole ne ya tuntubi jami’an tsaron Iran.

Kwamandan cibiyar sojan ta “Khatamul-Anbiyaa” Ali Abdullahi ya ce; Sojojin Iran ne suke kula da wannan mashigar,don haka muna yin kira ga dukkanin jiragen ruwan kasuwanci da su kaucewa karatar wannan mashigar ruwan,saboda kar su jefa kansu cikin hatsari.Haka nan kuma ya kara da cewa;

Muna gargadin masu goyon bayan Amurka da su ka kasance cikin fadaka, kar su yi abinda za su yi nadamar da ba ta amfani. Domin duk wani yunkuri da Amurka za ya yi da zummar sauya halin da ake ciki a wannan yankin, ba abinda zai haifar sai kara rikitar da lamurra.

Shi kuwa mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i cewa ya yi, ya kamata ace Amurka ta koyi darasi na cewa ba a yi wa Iran baranaza ko kurari da barazana.

A yayin taron manema labaru da ya yi a wannan Litinin din, Dr. Baka’i ya ce Dangane da batun tsaron Hurmuz, wanda yake da alhakin mayar da martani ya san abinda ya kamata ya yi domin kare tsaron kasar Iran.

Haka nan kuma ya ambato bayanin da ya fito daga cibiyar soja ta “Khatamul-Anbiyya” yana mai cewa; A duniyar nan babu  wanda yake gaskata cewa Amurka tana da halayya ta jin kai, kuma babu wanda ya gaskata cewa Amurkan za ta iya fitar da kanta daga cikin tsaka mai wuya da ta jefa kanta a ciki saboda yadda take maimaita kurakurai.

Haka nan kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su dorawa Amurka alhakin rashin tsaro, sannan ya kara da cewa; Gabanin kawo wa Iran hari, mashigar ruwan Hurmuz a bude take,kuma har yanzu jiragen ruwa za su iya wucewa ta ciki idan sun tuntubi bangarorin Iran da su ka dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted