A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Talata, wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon Ali Ammar ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ba za ta yi shiru kan duk wani hari da aka kai mata ba.
Bayanin wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya zo ne bayan wani mummunan harin bam da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan yankin Haret Hreik da ke yankin kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.
Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan wani gini da ke yankin Haret Hreik da ke kusa da asibitin Bahman a kudancin birnin Beirut, a daidai lokacin da rahotannin farko-farko ke tabbatar da shahadan mutane biyu da kuma jikkatan wasu da dama.