Hukumomin Saudiyya sun ce sama da mahajjata Miliyan daya da rabi sun isa kasar domin sauke farali, a yayin da ake ci gaba da tururuwa zuwa birnin Makkah gabanin fara gudanar da aikin hajji bana a wannan mako.
Hukumomin kasar sun ce sama da mahajjata ‘yan kasashen waje miliyan daya da rabi ne suka isa kasar zuwa ranar Talata, mafi yawansu ta jiragen sama daga sassan duniya.
Ana sa ran za a samu kari, kuma dubun dubatar ‘yan kasar Saudiyya da sauran mutanen da ke zaune a Saudiyya su ma za su bi su yayin da za a fara aikin hajjin a ranar Juma’a.
Hukumomin Saudiyya sun ce suna sa ran adadin maniyyatan bana zai zarce na shekarar 2023, lokacin da sama da mutane miliyan 1.8 suka gudanar da aikin Hajji.
Mahajjatan sun hada da Falasdinawa 4,200 daga yammacin gabar kogin Jordan.
Falasdinawa a zirin Gaza ba su samu zuwa Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana ba, saboda yakin da aka shafe watanni 8 ana gwabzawa tsakanin Isra’ila da Hamas.
A gobe Juma’a ne, maniyyata za su yi tattaki zuwa Mina, kafin daga bisani su nufi Dutsen Arafat wanda shi ne koluluwar aikin hajji, Daga nan su kwana a Muzdalifah, sai su nufi wurin jifan shaidan.
Hajjin na bana na gudan cikin tsannin zafi.
Hajji, wanda daya yake daga cikin shika-shikan Musulinci guda biyar, yana daya daga cikin manya-manyan tarurrukan addini a duniya.
Ana bukatar dukkan musulmi ya aiwatar da shi akalla sau daya a rayuwarsa idan fa har yana da karfin yin hakan.