Rahoton MDD : Isra’ila Ta Aikata Laifukan Yaki A Gaza

Wani sabon rahoto da MDD, ta fitar ya ce Isra’ila ta aikata laifukan yaki a lokacin yakin Gaza da aka faro tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. Rahoton wanda wani kwamitin bincike na kasa da kasa na MDD, ya fitar ya gano cewa mahukuntan Isra’ila na da alhakin “Laifukan yaki kan bil’adama” da suka […]

Maniyyata Na Isa Birnin Makkah Domin Fara Aikin Hajjin Bana

Hukumomin Saudiyya sun ce sama da mahajjata Miliyan daya da rabi sun isa kasar domin sauke farali, a yayin da ake ci gaba da tururuwa zuwa birnin Makkah gabanin fara gudanar da aikin hajji bana a wannan mako. Hukumomin kasar sun ce sama da mahajjata ‘yan kasashen waje miliyan daya da rabi ne suka isa […]

Qatar Ta Yi Kira Da A Dakatar Da Farmakin Da Isra’ila Ke Kai Wa Gaza Gaba Daya

Firaministan Qatar ya ce, duk wani mataki da za’a dauka game da kawoi kartshen yakin Gaza dole ya faro daga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta. Bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da MDD ke marawa baya, da kwamitin sulhu ya amince da ita, firaministan Qatar ya jaddada bukatar samar da mafita ta dindindin ga hare-haren […]

Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Yi Wani Abu Don Kawo Karshen Yaki A Gaza

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bukaci kasashen musulmi su yi wani abu a aikace don kawo karshen yaki a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawarsa ta wayar tarho da babban sakataren kungiyar kasashen Musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha a […]