Bayanai daga Mali na cewa, daruruwan mahalarta da suka halarci taron tuntubar kasa da ya kamata ya da shawarar hanyoyin warware rikicin tsaro da siyasa a kasar sun ba da shawarar da a tsawaita wa’adin mulkin sojoji da suka karbi mulki a shekarar 2020.
Har ila yau, sun nemi shugaban mulkin soja, Kanar Assimi Goïta, ya tsaya takarar shugaban kasa, bisa ga shawarwarin da aka karanta a karshen wannan “tattaunawar ta tsakanin ‘yan Mali” da gidan talbijin na gwamnatin kasar ya rawaito.
Tattaunawar ta ba da shawarar tsawaita lokacin mika mulki daga shekaru biyu zuwa biyar” da kuma bukatar Assimi Goïta ya tsaya takara a zaben shugaban kasa na gaba”, in ji sanarwar.
Tattaunawar ta kuma ba da shawarar “bude tattaunawar tare da kungiyoyin masu dauke da makamai,” in ji babban mai bayar da rahoto na kwamitin tattaunawar ta kasa Boubacar Sow.
Sojojin da suka karbi ragamar mulkin kasar a shekarar 2020, a shekarar 2022 sun yi alkawarin mayar da mulki hannun farar hula a watan Maris din 2024 bayan zabe.