Shugaban Kasar Iran Ya Jinjina wa Al’ummar Kasar Kan Juriyarsu Na Fuskantar Makiya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Hakuri da jajircewar al’ummar Iran sun yi galaba a kan makiya da suke kokarin kunna wutar tarzoma a kasar Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa: Dalilin kiyayya da kyamatar al’ummar Iran da makiya ke yi, sun samo asali ne sakamakon ire-iren gagaruman nasarori da ci gaba […]
Iran Ta Yi Allah Wadai Da Matakin Majalisar Dokokin Kasar Canada

Kasar Iran ta yi Allah wadai da matakin da majalisar dokokin Canada ta dauka kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci tare da sauran dakarun kasar sune ke da alhakin kare kan iyakokin kasar da tabbatar […]
Kasar Libiya Ta Shiga Sahun Masu Shigar Da Kara Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kasar Libiya ta bi sahun kasar Afirka ta Kudu a shigar da karar aiwatar da kisan kare dangi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta sanar da cewa: Kasar Libiya ta nemi shiga cikin sahun kasar Afirka ta Kudu a karar da ta shigar kan batun shari’ar zargin gwamnatin […]
Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Ta Yaba Wa Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Kasashen Larabawa sun yi maraba da kudurin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan batun neman sanya Falasdinu a matsayar cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya Matsayin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na amincewa da kudurin da ke goyon bayan bukatar kasancewar Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya ya samu karbuwa daga kasashen […]
Yakin Gaza Ya Cika Kwanaki 218 A Jere, Inda Yawan Shahidan Falasdinawa Suka Karu

Yakin Gaza ya cika kwanaki 218 cur yayin da ake ci gaba da samun karin shahidai sakamakon hare-haren bama-bamai kan yankin Hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Zirin Gaza suna ci gaba da gudana, inda suka ciki kwanaki 218 a jere, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun shahidai da jikkatan […]
Iran : Kuri’ar Babban Zauren MDD, Ta Nuna Yadda Amurka Ke zama Saniyar Ware Wajen Goyon Bayan Isra’ila

Iran ta yi maraba da matakin babban zauren MDD, na neman kwamitin sulhu ya amince da falasdinu a matsayin kasa mamba a majalisar. Jakadan dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya ce Tehran na maraba da amincewa da kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka na neman sake duba batun shigar […]
Babban Zauren MDD, Ya Bukaci Kwamitin Sulhu Ya Amince Da Falasdinu A Matsayin Mamba A Majalisar

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da ‘yancin Falasdinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar. Kudirin da UAE ta gabatar ya samu amincewar kasashe 143, yayin da 25 suka ce ba ruwan su, sai guda 9 da suka ki amincewa, da […]
Mali: ‘’Tattaunawa Ta Kasa’’ Ta Ba Da Shawarar Karin Shekaru Ga Mulkin Soji

Bayanai daga Mali na cewa, daruruwan mahalarta da suka halarci taron tuntubar kasa da ya kamata ya da shawarar hanyoyin warware rikicin tsaro da siyasa a kasar sun ba da shawarar da a tsawaita wa’adin mulkin sojoji da suka karbi mulki a shekarar 2020. Har ila yau, sun nemi shugaban mulkin soja, Kanar Assimi Goïta, […]
Gaza : Afirka Ta Kudu, Ta Sake Garzayawa Kotun ICJ, Kan Farmakin Isra’ila A Rafah

Kasar Afrika ta Kudu, ta sake komawa Kotun Duniya ta (ICJ), inda take neman kotun ta fitar da wani sabon umarni kan Isra’ila, wadda ta zargi a watan Disamba da laifukan kisan kiyashi. A wannan karon, Afirka ta Kudu ta nuna damuwa da halin da ake ciki a Rafah, inda sojojin Isra’ila ke dannawa. Pretoria […]
Shugaban Colombia Ya Yi Kira Ga Kotun ICC Da Ta Bada Sammacin Kama Netanyahu

Shugaban Colombia ya yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ta bayar da sammacin kame firaministan Isra’ila kan kisan kiyashi a zirin Gaza. Gustavo Petro ya fada a cikin wani sako na ‘’X’’ a ranar Juma’a cewa Benjamin Netanyahu ba zai dakatar da kisan gillar da ake yi ba kuma […]