Shugaban kungiyar malaman addinin musulunci ko –Council Of Ulema-na Tafawa Balewa a jihar Bauchi na tarayyar Najeriya Sheikh Dan’azuki Musa tafawa balewa, yayi kira ga kasashen musulmi da kuma sauran kasashen duniya da su dauki darasi a jajircewar JMI da turjiyarta ga HKI, a kuma matsayin hanya tilo ta kawo karshen HKI.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Sheikh Dan’azumi yana fadar haka a lokacinda yayi hira da shi a Bauchi. Sheikh Dan’azumi ya kara dacewa , gwamnatin Amurka ce bayan dukkan ayyukan ta’addancin da HKI take aikatwa a Gaza.
Ya ce kafin yakin kwanaki 12 da HKI ta kallafawa JMI, musulmi sun debe kauna da samun mafita ga matsalar al-ummar Palasdinu wacce aka dade ana fama da shi. Amma bayan nasarar da JMIta samu a kan HKI ta zamewa dukkan musulmi abin buga misali a turjiyara da kuma faskanta wadan nan makiya.
Don haka ya yi kara da dukkan musulmi da wadanda ba musulmi bas u dauki iran wannan dabarar ta JMI.