Majalisar Zaman Lafiya Ta Trump Da Kalubalen Nahiyar Afirka

An shiga wani zango a fagen siyasar kasa da kasa,wanda nahiyar Afirka ta sami kanta a gaban wani yanayi mai wuya da kalubale da zai

An shiga wani zango a fagen siyasar kasa da kasa,wanda nahiyar Afirka ta sami kanta a gaban wani yanayi mai wuya da kalubale da zai sa ta tsaya da kafafunta ta kare ‘yancinta, ko kuma akasin hakan.

Za a iya cewa nahiyar ta Afirka ce mafi rauni wajen fuskantar sauye-sauyen da suke faruwa a fagen siyasar kasa da kasa,musamman a wannan lokacin na Donadl Trump da ya fi zama mafi hatsari.

Idan za a iya tunawa a lokacin shugabancinsa na farko, Donald Trump ya yi maganganu na wulakanci da kaskantar da nahiyar ta Afirka. A wannan karon ma ba ta sauya zani ba, ta ma fi na baya muni saboda yadda ya yi wa Afirka ta Kudu karyar cewa tana yi wa fararen fata kisan kiyashi. Ya kuma zargi Nigeria da cewa tana kashe Mabiya addinin kiristanci. Bai kuwa tsaya anan ba, ya wuce gona da iri ya kai wa Nigeria hari da jajibiren kirsimeti.

A yayin taron Davos na tattalin arziki na 2026, Amurka ta bijiro da Shirin Donald Trump da ta kira; Majalisar Zaman Lafiya”. Haka nan kuma a wannan lokacin an gabatar da abinda aka kira; Tsarin tsaron kasar Amurka ( NDS 2026), wanda ya fito daga ma’aikatar yakin Amurka Pentagon. An kaddamar da shi ne a ranar 23 ga watan Janairu.

A cikin wannan Shirin na Amurka an ambaci sunan Afirka a wasu wurare kadan, tare da bayyanata a matsayin  wacce wasu yankunanta za su iya zama barazanar tsaro  ga Amurka. Wannan yana nuni da cewa, da idon barazana Amurkan za ta ci gaba da Kallon Afirka, saboda wai ‘yan ta’addar da za su  zamar mata barazana suna da mafaka a cikinta.

Siyasar Donald Trump Da Tsarin Duniya Mai Cike Hargitsi

Tsarin da duniya take tafiya a kansa wanda ya samo asali tun daga kare yakin duniya na biyu, an wayi gari yana da rauni saboda yadda wadanda su ka taka rawa wajen samar da shi, suna sa kafa su take shi a yanzu.

A cikin yanayi irin wannan, siyasar Donald Trump wacce take taka rawa wajen sake jefa duniya cikin hargitsi da yamutsi, ba a bai wa nahiyar ta Afirka wani muhimmanci. Za a iya ma cewa siyasar ta Trump ta fitar da nahiyar daga cikin duk wani lissafin cewa za ta taka rawa a fagen siyasar kasa da kasa.

Nahiyar ta Afirka ta sami kanta a cikin tsaka mai wuya; Na farko yadda Trump ya nuna rashin damuwa da ita, wani lokacin ma da nuna mata kyama.

Na biyu yadda kasashen turai su ka mayar da hankali wajen sake gyara gidansu, da rage dogaron da suke yi akan Amurka, don haka jingina da turai yana tattare da matsaloli.

Na uku: Kokarin neman sabbin abokai a cikin duniyar da kasashen turai suke da girman tasiri mafi girma ga nahiyar ta Afirka da kuma cin moriyarta na shekaru masu tsawo.

Fagen tsaro shi ne wanda ya fi zama mai sarkakiya, da ya sa  nahiyar ta Afirka take da bukatuwa gina karfinta na soja da kuma na tsaro, idan kuwa ba haka ba, to za ta fuskanci Karin tabarbarewar harkokin tsaro.

A aikace, Duniya tana fuskantar siyasar Donald Trump, kuma kasashen turai da suke gab da rasa kariyar da suke samu ta tsaro daga Amurka, babu aabinda  ya saura agaban su da ya wuce su samarwa kansu ‘yanci ta fuskar tsaron da kuma tattalin arziki. A cikin hali irin wannan ,dogaro da turai ba zai haifarwa nahiyar ta Aifka wani alfanu ba. Tun bayan yakin duniya na biyu nahiyar ta Afirka take gogoriyon ganin ta shiga an dama da ita a fagen siyasar kasa da kasa a cikin yanayi na yi ma ta adalci.

A daidai lokacin da nahiyar Turai take Kallon siyasar Trump a matsayin wata dama da za ta sa , ta yi kokarin tsayuwa da kafafunta, to ita nahiyar Afika tana zaman jira ne. Kuma yanayin da ake ciki a halin yanzu na karuwar tabarbarewar harkokin tsaro a cikin kasashe da dama na Afirka da kuma raguwar karfin gwamantoci.Haka nan kuma kasa rage tasirin kasashen waje a cikin mafi yawancin daidaikun kasashen nahiyar ta Afirka.

Majalisar Sulhu Ta Duniya:

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani da ya fito daga kasashen nahiyar ta Afirka dangane da Majalisar sulhu da Trump ya kafa.

Kasashen Afirka da su ka bayyana matsayarsu su ne; Moroko da Masar da suka ce suna son shiga cikinta.Sai dai wannan ba ya nufin cewa,  wadannan kasashen biyu sun bayyana matsayar tasu ne saboda kasantuwarsu, ‘yan Afirka, fiye da kasantuwarsu masu jinguwa da  Gabas ta tsakiya.

Watakila yadda shugaban na kasar Amurka yake yi wa Kallon Afirka da kaskanci,shi ya sa  shugabannin nahiyar suke dari-darin bayyana matsayarsu akan wannan sabuwar Majalisar ta zaman lafiya.

Ita dai wannan majalisar tun da farko an samar da ita ne, domin Gaza bayan farmakin 7 ga watan Oktoba a 2023 da kuma tsagaita wutar yakin da aka yi, bayan gushewar shekaru biyu ana yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.  Kuma daga cikin manufofinta da akwai aikewa da sojoji  zuwa cikin wannan yankin na zirin Gaza.

Don haka a matakin farko batun Gaza ba shi da muhimmanci ga nahiyar Afirka. Musamman kuma da ya zamana yana da alaka da Shi kanshi Trump.

Bugu da kari, wannan majalisar za ta ci gaba da zama a cikin wannan yanayi da manufarta ba ta fito fili sosai ba, domin ba ta da madogara ta dokar kasa da kasa, ko wata yarjejeniya da duniya ta amince da ita.

Da akwai fargaba a cikin nahiyar ta Afirkan kan abinda zai iya  faruwa da su a nan gaba, musamman bisa la’akari da yadda Trump din yake yi wa kawayensa na turai barazana,kamar Greenland.

Abinda kasashen na Afirka suke tsoro shi ne cewa kar Trump ya fake da batun kare; Kiristoci, ko “Fada da ta’addanci'” ko kuma ” Yi wa fararen fatar Afirka ta kudu kisan kiyashi” da zummar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen. Kasar Nigeria wacce ita ce mafi girma a cikin nahiyar ta Afirka tana a matsayin babban misali a gaban idanun dukkanin kasashen wannan nahiyar bayan da ya kai mata harin soja.www.hausatv.com

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted