Majalisar Kundin Tsarin Mulki A Chadi, Ta Tabbatar Da Zaben Mahamat Idriss Deby

Majalisar tsarin mulkin A kasar Chadi, ta tabbatar da zaben Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban kasar, da kashi 61% na kuri’un da aka kada,

Majalisar tsarin mulkin A kasar Chadi, ta tabbatar da zaben Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban kasar, da kashi 61% na kuri’un da aka kada, inda ya yi wa manyan abokan takararsa Succes Masra da Albert Pahimi fintinkau.

Majalisar ta yi watsi da karar da ‘yan takarar biyu suka shigar kan sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu.

Majalisar ta ce masu kalubalantar zaben sun gaza gabatar da hujjar cewa an yi magudi.

Kwanaki biyu bayan sanar da sakamakon zaben ne, babbar jam’iyyar hamayya ta kasar ta mika bukatar ta ga majalisar tsarin mulkin kasar inda take korafi game da sakamakon zaben da shugaban kasar na rikon kwarya Mahamat Idriss Deby ya samu.

Jam’iyyar Masra Success ta ce ta lashe zaben shugaban kasar da kashi 73% na kuri’un da aka kada, bisa ga kididdigar da ta yi, amma ba tare da fitar da cikakken bayani ba.

 

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments