MDD Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon yunwa a birnin El Fasher na Sudan Ofishin kula da ayyukan

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon yunwa a birnin El Fasher na Sudan

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya bayyana damuwarsa kan rahotannin da ke fitowa daga birnin El Fasher da ke arewacin Darfur, da ke cewa sama da mutane 60 sun mutu sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki cikin mako guda.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa ya fara tattara bayanan yunwa a sansanin Zamzam na ‘yan gudun hijira a Arewacin Darfur kimanin shekara guda da ta wuce, kuma ya jaddada cewa yana sa ran za a iya yada yunwa a wasu yankuna. A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa, abokan huldarta na cikin gida sun ba da rahoton mutane sama da 5,300 da ake zargi da kamuwa da cutar kwalara, inda mutane 84 suka mutu tun daga ranar 21 ga watan Yuni, yawancinsu a yankin Tawila, inda mutane 330,000 da suka rasa matsugunansu suke zaune a sansanin Zamzam da birnin El Fasher.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted