Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran Janar Hussain Mohibbi yana cewa a cikin makonni kimani biyu da suka gabata, wato daga ranar 6 zuwa 22 ga watan Yulin da muke ciki, bayan da Amurka ta sabawa takardan fahintar juna ta Islamabad, sojojin Iran sun yi masu barna da dama a yankin, kuma sun hada da .
Rada Rada Da Garkuwan Makamai, guda 7 a rundunoni da cibiyoyin kula da yaki. Cibiyoyin sadarwa ta tauraron dan’adam 3, na’urorin rada guda 6 samfurin Patriot, har sai da kai basa iya tare makamai masu linzami na kasar Iran.
Radoji 3, garkuwa sama a cibiyoyinsu, da wasu radoji guda 8 wadanda suke iya gani makamai masu hatsari da sauri. Sannan radoji masu kare sararin samaniyar sansanonin sojojin Amurka a yankin. Guda 7.
Sai kuma na’urorin rada 3 samfurin EPS, da wasu samfurin EPS 117 guda 2, Da radoji masu dogon zango 5, da wasu na kariya ko garkuwa guda 2. Sai kuma Taktikal Rada Complex guda 1.
Wasun sun hada da cibiyar gwaran jirage masu saukar ungulu 6, cibiyar bada tallafi 3, tankunan makamashi 12.
Rumbun makamai 17, wasu na makamaimasu linzami 6. Sai kuma jiragen MQc 9 6 da F-149 guda. Da wasu da dama, kamar yanda ya zo a shafin labarai na Tasnim.
Janar Mohibbi yace Iran ta lalata jiragen yakin Amurka 11 a cikin makonni biyu daga ciki har da jiragen yaki daban daban da masu saukar ungulu.