Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza

A wani bayanin hadin giwa wanda ministocin harkokin wajen kasashe 27 suka rattabawa hannu, ya bukaci firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bude hanya don shigoda abinci cikin gaza, don kawo karshen yunwa da ta bayyana a fili. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa daga cikin kasashen da suka sanyawa bukatar […]

Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji

Babban Hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila da kuma Amurka kan cewa duk wasu hare-hare kan kasar zai kara fushin sojojin kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na Iran Major General Abdolrahim Mousavi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da babban hafsan hafsoshin […]

Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen Lebanon da Iran basa daukan umurni daga Iran. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Dr Larijani yana fadar haka bayan kammala ziyaran aiki a kasar Iraki. Ya kuma kara da cewa kasashen Iraki da Lebanon suna […]

Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatarsa ce take kula da dukkan al-amuran da suka shafi shirin makamashin Nukliya na kasar, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta bukaci a jingine aiki da hukumar makamashin Nuikliya ta Duniya IAEA bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka suka […]

Araqchi: Kisan Kiyashi A Gaza Babban Abin Kunya Ne Ga Gwamnatocin Yammacin Turai

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunya ne shirun da gwamnatocin yammacin Turai suka yi game da muggan laifukan ‘yan sahayoniyya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya dauki kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa ‘yan jaridun Falasdinawa a matsayin wata shaida ta ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila […]

Larijani Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace

Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. […]

Iraki Ta Bukaci Tattaunawa Tsakanin Larabawan Yankin Tekun Farisa Da Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron […]

MDD Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon yunwa a birnin El Fasher na Sudan Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya bayyana damuwarsa kan rahotannin da ke fitowa daga birnin El Fasher da ke arewacin Darfur, da ke cewa sama da mutane 60 […]

Iran da Iraki sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro

Kasashen Iran da Iraki sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa a wannan  Litinin, dangane da tabbatar da tsaron kan iyakokin kasashen biyu, a ziyarar da babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya kai kasar Iraki. Larijani da mai baiwa gwamnatin Iraki shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji, […]

Masar ta yi gargadin daukar tsauraran matakai domin kare muradunta

Ministan harkokin wajen kasar Masar Badr Abdelatty ya yi gargadin cewa a shirye take ta dauki duk wani mataki na kare muradunta na iyakokin teku. Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Alkahira tare da ministan harkokin wajen kasar Ivory Coast, Léon Kacou Adom, wanda aka gudanar a wani […]

Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza

Ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta fita hayyacinta a yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, yayin da kuma yake nuni da cewa Italiya a shirye take ta bi sahun kasashen duniya wajen kakaba wa Isra’ila takunkumi. A cikin wata hira da jaridar La Stampa ta […]