Kakakin rundunar kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya bada sanarwan cewa, Amurkawa da suka halaka a fafatawar sojojin Amurka da Iran a cikin kwanaki 13 da suka gabata sun wuce 200.
Kamfanin dillancin labarab Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Hussain Mohibbi kakakin IRGC yana fadar haka a wata hira ta musamman da Tasnim, ya kuma kara da cewa, tun bayan da Amurka ta sabawa takardan fahintar juna ta Islamabad dakarun IRGC sun kai hare hare kan sansanonin Amurka akalla 8 a yankin inda take da tabbacin cewa ta kashe akalla sojoji fiye da 200 sannan wasu fiye da haka suka ji rauni.
Janar Muhibbi ya yi kira ga Amurkawa kada su yarda karyan da shuwagabanninsu suke fada masu dangane da yakin, saboda sun saba da karya, basa fada masu gaskiyan abinda yake faruwa.
.Daga karshe Janar Mohibbi ya bukaci Amurka ta kira taron yan jarida wadanda zasu ziyarci wadan nan wuraren da IRGC da sojojin Iran suka lalata don sanin irin barnan da aka yi masu.
Labaran da suke fitowa daga yankin kudancin kasar Iran dai sun bayyana cewa a daren jiya Lahadi, dai babu wasu hare haren da sojojin Amurka suka kawo yankin.
Amurka da HKI ne suka fara yakin a kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrayru da nufin kifar da gwamnatin JMI da kuma kwace iko da Ita.