Iran Tace Babu Mafita A Yaki Tsakanin Yamen Da Saudiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana cewa rikici tsakanin yemen da Saudi aba za’a iya warware shi a yaki ba, don

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana cewa rikici tsakanin yemen da Saudi aba za’a iya warware shi a yaki ba, don haka yayi kira ga bangarorin biyu su koma kan teburin tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran Mehr News na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar haka, a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, yana bada shawarar kasashen biyu su sake komawa kan tsarin da suka amince a baya na kawo karshen yaki a tsakaninsu, su kuma aiwatar da su kamar yanda suke.

Baghae ya bayyana cewa akwai bukatar a kawo karshen wahalar da mutanen Yemen suka sha, fiye da shekaru 12 da suka gabata, kuma suna da hakkin tada hankali don ganin an maida hankali a kansu.

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted