Mahukuntan Yankin Tigray Sun Zargi Addis Ababa Da Shelanta Yaki Akan Yankin

Tsawon watanni aka shafe bangaren ƴan tawayen na Tigray da kuma gwamnatin kasar ta Habasha na girke mayaka a kan iyakar yankin na Tigray lamarin
Taswirar Habasha

A jiya Asbar ne dai mahukuntan yankin na Tigray su ka zargi gwamnatin tarayyar Habasha da cewa sun shelanta sabon yaki akansu da hakan yake kara jefa yankin cikin zullumin sake dawowar wani sabon yakin.

َA wata sanarwar da kungiyar ‘yanto yankin na Tigray ( TPLF) ta fitar ta ce sojojin gwamnatin tarayya sun yi amfani da manyan bindigogi wajen kai hari a yammacin yankin a kusa da iyaka da kasar Sudan.

Bayan watanni da killace yankin da sojojin gwamnatin tarayya su ka yi, da kuma kai hare-hare da jiragen sama marasa matuki, yankin gwamnatin ta bude cikakken yaki akan yankin.

Tsawon watanni aka shafe bangaren ƴan tawayen na Tigray da kuma gwamnatin kasar ta Habasha na girke mayaka a kan iyakar yankin na Tigray lamarin da ya sanya kowanne bangare zargin dan uwansa da kokarin tayar da rikici.

Wasu mutane sun shaidawa AFP cewa har zuwa safiyar yau Lahadi ana ci gaba da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu kuma dukkaninsu na amfani da manyan makamai a yammacin na Tigray yankin da ake takaddama akan shi tsakanin mahukuntan Habasha da ƴan gwagwarmaya masu ikirarin kishin yankin Amhara.

A 2022 ne bangarorin biyu su ka rattaba hannu akan yarjejeniyar kawo karshen yaki a Pretoria na kasar Afirka Ta Kudu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted