Wata tawaga a ma’aikatar tsaron Amurka {Pentagon} tana tattauna batun janyewar sojojin Amurka daga kasar Nijar
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da cewa: Wata tawagar manyan jami’an Amurka ta gudanar da wani zaman tattaunawa a Nijar a ranar Larabar da ta gabata domin yanke shawarar batun janyewar sojojin Amurka da shugabannin sojin Nijar suka nema, a kasar da ke yammacin Afirka.
Kimanin sojojin Amurka 650 da wasu daruruwan ma’aikatan kwangila ne Amurka ta jibge a kasar da ke tsakiyar Afirka.