Search
Close this search box.

Ma’aikatar Lafiya : Adadin wadanda suka yi shahada a Gaza ya zarce 35,000

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a Gaza ya haura 35,000 a yakin da Isra’ila ke yi a

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a Gaza ya haura 35,000 a yakin da Isra’ila ke yi a kan  yankin da ta yi wa kawanya.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a yau Lahadi, ta ce tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da farmakin a ranar 7 ga watan Oktoba, an kashe akalla mutane 35,034, ciki har da yara 15,000. Bayanin Ya kara da cewa mutane 78,755 kuma sun jikkata.

Sanarwar ta kara da cewa har yanzu Falasdinawa da dama na makale a karkashin baraguzan gine-gine da ma’aikatan ceto da na agaji da ma’aikatan agajin gaggawa da jami’an farar hula ba su samu damar kai wa gare su ba, saboda dimbin barna da kuma rashin kayan aikin tono.

Bayan shafe watanni 7 Isra’ila tana kai hare-hare babu kakkautawa, a halin yanzu gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kara tsananta wadannan hare-hare, inda ta umarci sojojin yahudawan da su kai farmaki a kudancin garin Rafah, inda aka tsugunnar da  Falastinawa  miliyan 1.5 da suka rasa muhallanu.

Wannan matakin dai ya janyo fargaba a duniya kan yadda dakarun gwamnatin yahudawan ke kara zage damtse wajen ci gaba da yin  kisan kiyashi a kan fararen hula a Gaza.

A yanzu dai kasashen duniya sun gamsu da cewa Isra’ila ba ta da niyyar yin aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta dindindin a Gaza, kuma yakin da suke yi na kisan kare dangi zai ci gaba har sai sun cimma manufa ta karshe ta rusa yankin Gaza baki daya, da kuma halaka sauran dukkanin Falasdinawa da suka rage a raye a cikin yankin, duk da sunan yaki da Hamas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments