Ma’aikatar harkokin wajen Iran din ta gayyato jakadan kasar Birtaniya ne dake nan Iran domin nuna masa kin amincewa da matakin da matakin da kasarsa ta dauka na kama wani dan asalin kasar Iran da mi ka shi ga Amurka bisa zargin cewa yana aiki domin kaucewa takunkumin da aka kakabawa kasar.
Kamfanin Dillancin Labarun “Irna” na Iran ta ambato wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen kasar yana cewa; An gargadi jakadan na Birtyaniya akan abinda kasar tasa ta yi, wanda kuma ya sabwa doka.
HJar ila yau jami’in ma’aiaktar harkokin wajen na Iran y ace;kasarsa za ta yi duk abinda za ta iya yi domin ganin an dawo da dan Iran din zuwa gida.