Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Cewa: Ana Ci Gaba Da Tafka Muggan Laifukan Yaki A Gaza

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta jaddada cewa: Ci gaba da yakin Gaza laifi ne ga dukkan bil’adama Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta jaddada cewa: Ci gaba da yakin Gaza laifi ne ga dukkan bil’adama

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Ci gaba da yakin Gaza da kuma kashe-kashe da raunata dubban daruruwan Falasdinawa, yakin wuce gona da iri ne da kuma laifi kan dukkanin bil’adama da kuma keta haddin jan layuka na shari’a.

Kan’ani ya rubuta a shafinsa na sada zumunta a dandalin “X” cewa: A lokacin da ‘yan majalisun dokokin Amurka suke tafawa fira ministan gwamnatin haramtacciyar hasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya kasance makashin mata da kananan yara, kuma yana neman karin tallafin makamai, baya ga jiragen saman yaki da suke luguden wuta kan makarantu da suka zame sansanonin ‘yan gudun hijira da kuma kan sansanonin ‘yan gudun hijira da suke yankin Zirin Gaza, lamari ne da ke tabbatar da cewa: Jami’an Amurka ne suka umurce shi tare da karfafa shi kan aikata muggan laifukansa.       

Ya kara da cewa: Kisan kiyashin da aka aiwatar a kan makarantar Sayyidah Khadija da ke Deir al-Balah, wanda ke dauke da dubban ‘yan gudun hijirar Falasdinawa, shi ne aikin baya-bayan nan da gwamnatin Amurka ke nuna goyon baya ga yahudawan sahayoniyya ba tare da wani sharadi ba, da kuma tafi ga fira ministan yahudawan mai aikata muggan laifukan yaki a majalisar dokokin Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments