Libya : An Fara bincike kan kisan Saif Al Islam Gaddafi

A Libiya an fara gudanar da bincike kan kisan Saif Al Islam da ga tsohon shugaban kasar mirigayi Muammar Ghaddafi. Wasu ‘yan bindiga da ba

A Libiya an fara gudanar da bincike kan kisan Saif Al Islam da ga tsohon shugaban kasar mirigayi Muammar Ghaddafi.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe Saif Al Islam Gaddafi a birnin Zintan ranar Talata.

Babban Lauyan Libya al Siddiq al Sour ya fara bincike a wannan Laraba kan kisan Saif Al Islam Gaddafi.

Wata sanarwa da Ofishin Bincike na Babban Lauyan ya fitar ta ce masu bincike “sun binciki wurin da aka kashe Saif Al Islam, sun tattara kayayyaki, sun kuma yi hira da shaidu, da duk wanda zai iya bayar da bayani game da lamarin.”

Likitoci sun kuma duba gawar Saif Al Islam, in ji ofishin babban lauyen.

Binciken farko ya nuna cewa Saif Al Islam ya fuskanci harbin bindiga wanda ya yi sanadiyyar raunata mutane da dama,” in ji sanarwar.

Kafafen yada labaran Libya sun ruwaito cewa kisan ya faru ne a gidan Saif al Islam kuma mutane hudu da ba a san ko su waye ba ne suka aikata shi, sun kara da cewa an kashe kyamarorin sa ido a wurin kafin harin.

Tuni aka fara zargin hannun kasashen waje a lamarin.

Kisan na Saif Al Islam na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye shiryen zabubuka a kasar.

Saif Al Islam kuma yana daga cikin wadanda ake ganin zasuyi tasiri a zaben.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments