Sojojin Amurka kimani 8 ne suka ji rauni a ci gaba da fafatawa da Amurka take yi da Iran a mashigar ruwa ta Hurmuz.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto NBC News na Amurka na fadar haka a ranar Lahadi jiya, ta kuma kara da cewa, wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta ta fada mata kan cewa sojojin sun ji rauni ne tun makonni biyu da suka gabata a lokacinda suka fafatawa sojojin Iran a mashigar ruwa ta Hurmuz.
Kafin haka dan rahoton fox News ya bada labarin cewa makaman JMI sun fada kan jirgin yakin Amurka a mashigar ruwa ta Hurmuz. Kuma sojojin Amurka da dama sun ji rauni.
NBC News ta tabbatar da cewa wadanan sojoji 8 ne suka ji rauni a wadan nan hare hare.
Daga cikin raunukan da suka ji har da shakan hayaki masu yawa, wadanda suke jawo matsaloli a kwakwalensu.
Sannan ta kara da cewa makaman IRGC sun fada a kan jirgin ne a ranar 14 ga watan Satumban da muke ciki.kamar yadda wani jami’an gwamnati wanada ba’a bayyana sunansa ba ya fada.
Hukumar yaki da Pentagon ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suka ji rauni a zuwa yanzun tun bayan fara yaki da Iran sun kai 861.
Sojojin Iran suna da cikekken iko da mashigar ruwa ta Hurmuz tun bayan fara yakin a ranar 28 ga watan Fabrayrun da ya gabata.