A yau Litinin ne yahudawa ‘yan share wuri zauna a karkashin jagorancin ministan tsaron kasa, Ben Gafir su ka kutsa cikin harabar masallacin Kudus tare da kariyar ‘yan sandan sahayoniya.
Kantomar birnin Kudus, ya sanar da cewa; ‘yan sanda sun rufe hanyoyin da suke shiga cikin tsohon birnin da kuma hanyoyin da su ka zagaye da masallacin Kudus.
Kutsen masallacin kudus din da ‘yan share wuri zaunar su ka yi, yana zuwa ne a lokacin da suke bikin addini da ya shiga cikin kwanaki na uku.
Kantomar birnin na kudus ta kuma ce; ‘Yan share wuri zauna din sun rika yin kide-kide da raye-raye a cikin farfajiyar masallacin na kudus.
Itmar Ben Gafir da ya shiga cikin masallacin na Kudus ya bayyana cewa: “Wannan wajen namu ne dake Aqsa, kuma mun mayar da rayuwar frusunoni masu barna zama cikin matsananciyar wahala.”
Haka nan kuma ya ce; “Al’ummar Isra’ila tana kan hanyarta ta samun cikakkiyar nasara, za kuma mu yi ibada a yau a cikin Aqsa, wanda shi ne wuri mafi muhimmanci ga yahudawa.”
Har ila yau ministan tsaron HKI Ysra’il Kats ya jagoranci wata zugar ta ‘yan share wuri zauna da sun kai dubbai su ka kutsa cikin masallacin na Kudus.
Kutsen cikin masallacin Kudus ya zama Ruwan dare da yan sahayoniya suke yi daga lokaci zuwa lokaci, sai dai a bayan nan ya yi kamari, lamarin da yake barazana ga ginin masallacin da shi ne alkiblar musulmi ta farko.