An gudanar da gangani da kuma Zanga-zanga a cikin garuruwa 45 a fadin kasar Moroko domin nuna goyon bayan al’ummar Falasdinu da kuma kin amincewa da batun kulla alakar diplomasiyya a tsakanin kasar da Haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kungiyar dake nuna goyon bayan batutuwan da su ka shafi al’umma wacce ta shirya ganganin da tarukan da kuma Zanga-zangar ta ce; ana gudanarda tarukan ne a wurare 76 a cikin birane 45. Haka nan kuma ta ce; taken da ake bayarwa shi ne; Kin amincewa da kulla alaka da Isra’ila.
Daga cikin garuruwan da ake yin gangamin da tarukan da akwai; Ribat,Daral-Baidha’a, Marrakish, Danja da Faris. Haka nan kuma garuruwan Agadir, Wajdah, da Qunaidhara,sai kuma Tadhawan.
Al’ummar Kasar ta Moroko suna nuna kin amincewa ne da matakin bayan na da gwamnatin Moroko ta dauka na musayar jakadu da Haramtacciyar Kasar Isra’ila da kuma bude ofisoshin jakadanci.
Masu gangami da zanga-zangar dai sun daga tutocin Falasdinu da kuma kwalaye da suke dauke da yin kiran kawo karshen yakin Gaza da dakatar da alaka da “Isra’ila.”. Har ila yau sun rika bayar da taken nuna kin yarda da bude ofishin jakadancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Ribat, da kuma bude ofishin Moroko a Tel Aviv.
An yi gangamin ne daga ranar 25 ga watan Satumba zuwa 27 gare shi.