Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta sake fadawa yaki da Amurka idan ta tilastawa kasar hakan, amma tare da bude kufar tattaunawa idan tana so.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake yin hira da tashar talabijan ta NBC News ta kasar Amurka a lokacinda yake halattar babban taron babban zauren MDD karo na 81 a birnin NewYork na kasar Amurka. Yace Iran zata ci gaba da tsayawa daram kan matsayinta ko da kuwa hakan zai kaiga shafe kasar daga bdoron kasa kamar yanda Trump yake riyawa.
Yace a dai dai lokacinda muke yake a duk lokacinda Trump ya zabi tattaunawa kofar tattaunawa a bude take.
Arachi ya bayyana haka ne bayan da Jaridar world Treet Journal ta nakalto cewa mai yuwa Trump ya koma fagen fama bayan zabubbukan majalisar dokokin kasar a cikin watan Nuwamba mai zuwa.